Fasa gidan yari a Damaturu

Infotaula d'esdevenimentFasa gidan yari a Damaturu
Iri aukuwa
Kwanan watan 2 ga Yuni, 2012
Wuri Jihar Yobe
Adadin waɗanda suka rasu 8

Fasa gidan yarin Damaturu dai wani hari ne da wasu ƴan bindiga su 40, da ake kyautata zaton ƴan ƙungiyar Boko Haram ne suka kai a gidan yarin Jimeta da ke garin Damaturu babban birnin jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya. Ana tunanin harin wani yunƙuri ne na ceto ƴan kungiyar Boko Haram ɗin da ke ɗaure.[1][2] Kimanin fursunoni 40 ne suka tsere daga gidan yarin; fursunoni bakwai da mai kula da gidan yari ɗaya sun mutu.[3] Fursunonin da suka tsere yawancinsu ƴan tawayen ne.[4]

  1. "Boko Haram prison break: Radical sect frees 40 in Nigeria". Huffington Post. Archived from the original on 2014-12-29.
  2. "BBC News - Nigeria unrest: Inmates escape in Damaturu jail attack". BBC News.
  3. "Boko Haram kills eight frees 41 inmates in Damaturu prison attack". Pointblank News.
  4. "Boko Haram invades Damaturu Prison, frees 40 prisoners". Vanguard News.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search